Jump to content

Dandalin Sada Zumunta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sake dubawa tun a 08:49, 12 Oktoba 2024 daga Bashir nuhu usman (hira | gudummuwa) (NAsa photo)
(bamban) ←Canji na baya | Zubi na yanzu (bamban) | Canji na gaba → (bamban)
Dandalin sada zumunta
economic activity (en) Fassara, industry (en) Fassara, hanyar isar da saƙo, genre (en) Fassara, specialty (en) Fassara, field of study (en) Fassara da type of mass media (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na hanyar isar da saƙo da virtual place (en) Fassara
Karatun ta media studies (en) Fassara, interaction science (en) Fassara, digital media (en) Fassara, media sociology (en) Fassara da zamantakewa
Matsalar da zata iya haifarwa gurɓataccen bayani, misinformation (en) Fassara da catfishing (en) Fassara
Gudanarwan mai kula da dandalin sada zumunta da ƙwararre a dandalin sada zumunta
Uses (en) Fassara Yanar gizo
Dandalin Sada Zumunta

Dandalin sada zumunta, ta kasance wata mahaɗa ce da dubban mutane daga sassan duniya su ke haɗuwa domin sada zumunci da kuma gudanar da sauran harkokinsu na yau da kullum.

Dandalin sada zumunta ya ƙunshi kafofin sadarwa kamar; Facebook, Twitter, WhatsApp, Instagram da sauransu. Kasancewar ire-iren wayoyin hannu da muke amfani da su a wannan zamani su na ɗauke da manhajoji (apps) wanda sunsha banban da wayoyin shekarun da su ka gabata, ya sa dandalin sada zumunta ya ƙara bazuwa a sassan duniya, domin zaiyi wahala a samu waya ƙirar Android ba a samu ɗaya daga cikin manhajojin kafafen sadarwa ba.

Amfani dandalin da rashinsa

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da dandalin sada zumunta, shiyasa kowa ya na da hanyar da yake amfani da dandalin. Wasu daga cikin hanyoyin sune;

- Sada Zumunci: Mutane da dama su na amfani da dandalin sada zumunta domin sada zumunci tare da ƴan uwa da abokan arziki musamman waɗanda su ke nesa, dandalin ya na haɗa zumunci tsakanin mutanen da basu san juna ba ko haɗuwa da juna a zahiri ba har a zama tamkar ƴan uwa, ko kuma soyayya ta ƙullu a tsakani.

- Kasuwanci: Kasancewar dandalin sada zumunta matattara ce ta dubban mutane, hakan ya sa wasu ƴan kasuwa su ke amfani da dandalin ta hanyar siye da siyarwa, su na shiga su tallata hajojinsu domin neman masu siye, wasu kuma su na shiga su nemi abinda su ke bukatar siya.

- Labarai: Kasancewar yadda hankalin yawancin jama'a ya karkata ga dandalin sada zumunta, ya sa yawancin Gidajen Jaridu, Rediyo da Telebijin su ke amfani da dandalin domin saka labarai game da halin da duniya take ciki da sauran shirye-shiryensu. Wannan ya sa mutane su na shiga domin sanin halin da duniya take ciki, da samun labarai game da harkokin yau da kullum.

- Neman Ilimi: Mutane su na amfani da dandalin sada zumunta domin neman ilimin addini, boko, kasuwanci, zamantakewar yau da kullum da suransu.

Waɗannan wasu daga cikin hanyoyin amfani da dandalin sada zumunta kenan.

Sai dai wani abin takaici shine, yadda wasu ɓata gari su ke neman canza alƙiblar wannan dandali na sada zumunta zuwa dandalin tada husuma. Domin yanzu duk wani labari na tashin hankali da raba kawunan al'umma daga dandalin sada zumunta ya ke fitowa. Wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu wajen tada husuma a dandalin sada zumunta sune;

- Labaran Ƙarya: Kasancewar hankulan mutane sun karkata wajen neman labarai a kan halin da duniya ta ke ciki, wannan yasa wasu ɓata gari su ke amfani da wannan dama wajen tada zaune tsaye ta hanyar watsa labaran ƙarya. Mutum ya na kwance a ɗakinsa zai ƙirƙiro labarin ƙarya, wasu lokutan har da hotuna da bidiyoyi na ƙarya ya watsa a dandalin sada zumunta a matsayin labari. Wannan yana tasiri sosai wajen tunzura jama'a da zai haifar da tashin hankalin da za a iya asarar dukiyoyi da rayuka.

- Rikicin Addini: Wasu ɓata gari su na amfani da dandalin sada zumunta wajen raba kawunan al'umma, musamman tsakanin waɗanda su ke da banbanci a ɓangaren addini, ta hanyar watsa maganganun da basu dace ba akan addinai mabanbanta. Wannan yana tasiri sosai wajen raba kawunan al'umma da zai iya sanadiyar rashin zaman lafiya a tsakanin al'umma.

- Rashin Daraja Mutane: Wasu mutane su na amfani da dandalin sada zumunta wajen furta baƙaƙen maganganu, habaici, har da zage-zage ga waɗanda su ka samu rashin jituwa ko kuma ra'ayinsu yasha banban da nasu a ɓangaren addini, siyasa, ƙabila da sauransu.

Idan muka lura, zamu ga duka waɗannan su na faruwa a dandalin sada zumunta a yanzu, wanda wannan yasha banban da sunan wannan dandalin wato dandalin sada zumunta.

Ina Mafita?

Mafita itace mutane su rinƙa lura da abubuwan da ake sakawa a dandalin sada zumunta, su tabbatar da sahihancin abinda su ka gani a dandalin kafin su yi aiki dashi domin gujewa duk wata matsalar da zata biyo baya.

Sannan ya kamata gwamnati ta saka ido akan ire-iren waɗannan matsalolin musamman hanyoyin da ake bi wajen tada zaune tsaye da raba kawunan al'umma, musamman a wannan lokaci da ake fuskatar barazanar tsaro.