Kasuwa
kasuwa | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | market (en) , wuri, wuri da kasuwa |
Hashtag (en) | Wochenmarkt da Market |
Kasuwa, wani keɓantaccen guri ne da ake tanada don haɗuwa a yi cinikayya wato saye da sayarwa. Gurin hada-hadar kasuwanci [1] Wanda ita kasuwa tana haɗa mutane daban-daban daga wurare mabam-banta da ƙasashe daban-daban kuma ita kasuwa kusan komai akwai a cikinta. Jam'in kasuwa shi ne kasuwanni haka kuma wanda yake harkar.
kasuwanci ana ce masa ɗan kasuwa. Ana yi wa kasuwa kirari da "kasuwa akai maki tilas in an ƙiya a kai maki babu" kasuwanni iri-iri ne akwai kasuwar dabbobi akwai kuma kasuwar hatsi da dai sauran kasuwanni. Akwai kasuwa da ake cinikayya ta cikin ƙasa akwai kuma ta ƙasa da ƙasa.[2]
Bunkasa Tattalin arziki
[gyara sashe | gyara masomin]Kasuwa dai baya ga bunkasa tattalin arzikin waɗanda ke yin kasuwancin, tana kuma bunkasa ko taimaka wa gwamnati ta hanyar samun kuɗaɗen shiga ta sigar biyan haraji daga `yan kasuwa. Akan bayar ko haraji a duk sati ko wata ko kuma ya danganta da yadda gwamnati ta tsara za ta rinka amsa a lokacin da ta tsara.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-56073011
- ↑ https://podcasts.google.com/feed/aHR0cHM6Ly93d3cucmZpLmZyL2hhL3NoaXJ5ZS1zaGlyeWUva2FzdXdhbmNpL3BvZGNhc3Q/episode/NzJiODY0ZDYtNDUwOC0xMWViLTk4NDEtMDA1MDU2YmZmNGE4?sa=X&ved=0CAYQkfYCahcKEwjg1f-pkYDwAhUAAAAAHQAAAAAQAQ